1 Corinthians 3

1Amma ni, yan’uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu. 2Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba.

3Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane? 4Domin in wani ya ce, “Ina bayan Bulus,” wani kuma ya ce, “Ina bayan Afollos,” ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba? 5To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka.

6Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma. 7Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman.

8Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa. 9Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma.

10Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin. 11Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu.

12Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka, 13aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi.

14Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada; 15amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta.

16Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku? 17Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke.

18Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama” wawa” domin ya zama mai hikima. 19Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima a cin makircin su.” 20Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.”

21haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne, 22Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne, Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.

23

Copyright information for HauULB